Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, baya ga babban zarafin neman samun bunkasuwa da yankin Asiya da Turai ke da shi, hatta yana kuma fuskantar kalubale sosai, musamman ma a fannin ta'addanci da batun 'yan gudun hijira.
A saboda haka, ya kamata bangarorin su tabbatar da matsayi daya da aka cimma a gun taron kasashen Asiya da Turai domin girmama juna da tattauna batun cikin ruwan sanyi tare da inganta hadin gwiwa a tsakaninsu ta yadda za a daga matsayin hadin gwiwar dake tsakaninsu.
Bugu da kari, Li Keqiang ya bayyana yanayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, inda ya bayyana cewa, a farkon rabin wannan shekara, kasar Sin ta gudanar da tattalin arzikinta yadda ya kamata a lokacin da take fuskantar kalubale da dama, wannan ya yi daidai da abin da aka yi hasashe. Kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a cikin gida tare da bude kofa ga kassshen waje da kara gyara tsarin tattalin arzikin kasar. Sin da niyyar cimma burinta na wannan shekara a fannin tattalin arziki, domin kiyaye saurin bunkasuwarsa, ta yadda za ta ba da gundummawa ga bunkasuwar tattalin arziki da kiyaye zaman lafiya a yankin Asiya da Turai.(Lami)