in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wasu kungiyoyin ta'addanci dake karfin gudanar da manyan ayyuka a yankin Sahel, in ji wani janar din Faransa
2016-09-14 10:34:09 cri
Kungiyoyin ta'addanci dake yankin Sahel ba su da karfin gudanar da manyan ayyuka, da zasu basu damar kwace wani gudan birni da kuma kafa tutarsu, in ji sabon komandan dakarun Barkhane, dake hedkwata a Mali, janar Francois-Xavier De Woillemont a ranar Talata a birnin Ouagadougou.

A yankin Sahel, babu kungiyoyin ta'addanci da suke da karfin gudanar da manyan ayyuka. Amma hakan ba ya nufin cewa an warware matsalar, wannan yana nufin cewa ayyukan dakarun G5 dana Barkhane sun cimma nasarorinsu, in ji komandan dakarun Barkhane, bayan wata ganawa tare da shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore.

Sabanin abin da ake tsammani, dakarun G5 dake kunshe da sojojin Burkina Faso, Chadi, Mauritaniya, Nijar da Mali tare da Barkhane sun samu muhimman nasarori kan kungiyoyin ta'addanci, in ji janar din na Faransa.

A cewarsa, 'yan ta'adda basu wani karfin dabarun yaki. Wato karfin su kwace wani birni da kafa tutarsu. Har yanzu sun kasance babbar matsala, kamar dukkan 'yan ta'addan duniya, amma basu da abin da ake kira masana'antar ta'addanci musammun ma a arewacin Mali.

Yawancin kasashen da ke yankin Sahel sun fuskanci hare haren ta'addanci a shekarun baya bayan nan, tare da tilasta wa hukumomin kasashen karfafa yaki da rashin tsaro, tare da taimakon Faransa.

Tun kaddamar da ita a ranar daya ga watan Augustan shekarar 2014, bayan ayyukan dakarun Serval da Epervier, Barkhane ta kasance wata tawagar dakarun kasar Faransa dake aiki a yankin Sahel, da ke manufar yaki da kungiyoyin ta'addanci da kungiyoyi masu makamai dake dukkan yankin Sahel. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China