Mr. Liu wanda ya bayyana hakan yayin zaman kwamitin tsaro game da yankin na Sahel wanda ya gudana a jiya Laraba, ya ce akwai matukar bukatar hada karfi da karfe wajen tallafawa yankin na Sahel, don fita daga mawuyacin halin rashin tsaro da karancin matakan ci gaba.
Liu ya kuma ja hankalin masu ruwa da tsaki game da halin da kasar Mali ke ciki, yana mai fatan za a kai ga aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya, da sulhu, wadda aka kulla cikin watan Yunin wannan shekara da muke ciki. A cewarsa ya dace MDD ta kara kwazon, wajen ganin an shawo kan matsalolin ta'addanci a yankin baki daya.
Game da samar da ci gaba kuwa, Mr. Liu ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen na yankin Sahel su yi amfani da kudurorin samar da ci gaba na shekarar 2030, wajen fidda tsare-tsaren bunkasuwa gwargwadon bukatun kasashen su.
Da yake tsokaci game da dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC wanda za a bude nan da 'yan kwanai, jakadan na Sin ya ce taron wata dama ce ga sassan biyu, ta tsara manufofin ci gaban dangantakar su a tsahon shekaru 3 masu zuwa.(Saminu Alhassan)