in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD mai kula da harkokin siyasa zai halarci taron kolin Sahel
2015-11-20 09:59:42 cri
Mataimakin babban magatakardan MDD mai kula da harkokin siyasa Jeffrey Feltman zai halarci taron kolin kasashen yammacin Afirka ko G5 a takaice, taron da zai gudana a birnin N'djamena na kasar Chadi.

Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan ga manena labarai, ya ce, ana sa ran jami'in zai sadu da manzon musamman na babban sakataren MDD mai kula da yankin Sahel Hiroute Guere Sellassie, kana ya gabatar da jawabi a madadin babban sakataren MDD.

Dujarric ya ce, an wallafa kashi na biyu na rahoton babban sakataren MDD dangane matakan da ya kamata a aiwatar a yankin na Sahel,mako guda gabanin taron kolin da aka shirya gudanarwa game da yankin.

Mr. Ban ya bayyana bacin ransa game da makomar miliyoyin matasa sakamakon yadda al'amura suka tabarbare a yankin. Ya kuma tabo yanayin tsaro sakamakon tashin hankalin da ke da ci gaba da faruwa a kasashen Mali da Libya da bullar kungiyoyin 'yan ta'adda kamar Boko Haram da Al Qa'ida da fataucin miyagun kwayoyi.

A watan Fabrairun shekarar 2014 ne shugabannin kasashen na G 5 suka amince a taron da suka yi a Nouakchott na kasar Mauritania na kafa wannan kungiya, inda suka jaddada bukatar mayar da hankali kan harkokin tsaro da raya yankin,martaba tsarin demokiradiya, kare 'yancin bil-adam da yayata kyakkyawan mulki.

Rahotanni na nuna cewa, kimanin mutane miliyan 4 da dubu 500 ne suka bar gidajensu a yankin. MDD dai na fatan warware abubuwan da suka haddasa matsalar tsaro a yankin karkashin sabon jam'in da ta nada.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China