Chambas, wanda kuma shi ne shugaban ofishin MDD na yammacin Afrika da yankin Sahel, ya bayyanawa kwamitin sulhu na MDD game da halin da ake ciki a yammacin Afrika da Sahel cewa, matsalolin da suka shafi rashin aikin yi, da rashin adalci sun taimaka wajen haddasa yawaitar kungiyoyin tada kayar baya a yankunan.
Ya bukaci kasashen duniya su hada karfi da karfe wajen rigakafin barkewar rikice rikice da kuma dakile rikicin tun a matakan farkon.
Yace kasashen yammacin Afrika da yankin Sahel, dole ne su maida hankali wajen samar da hanyoyin tattara bayanan sirri domin yaki da kungiyoyin tada kayar baya kamar su Boko Haram, wadanda suke kaddamar da hare haren ta'addanci a kasashen Najeriya da Nijer da Kamaru.(Ahmad Fagam)