Mai magana da yawun Toby Lanzer, jami'ar dake kula da sashen jin kai na ofishin MDD, Farhan Haq, ya fada wa taron manema labarai cewar, jerin gwanon matsaloli da suka hada da matsalar sauyin yanayi da matsanancin talauci da karuwar yawan jama'a da matsalar tashin hankali da tabarwarewar tsaro su ne suka jefa rayuwar al'ummomin yankunan cikin matsanancin hali.
Mai yiwuwa ne a shekarar 2016, mutane sama da miliyan 23 za su iya rasa don abin da za su kai bakin su, don haka akwai bukatar a baiwa al'ummar agajin gaggawa wajen samar musu da abinci, musamman don gujewa jefa rayuwar kananan yara 'yan kasa da shekaru 5 kimanin miliyan 5 da dubu 900 daga fadawa cikin garari.
Ko a ranar Talatar da ta gabata sai da kwamitin tsaro na MDD ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da kariya ga al'ummar kasar Libya da kewayen ta daga fuskantar barazanar hare haren mayakan al-Qaida.
Wata sanarwar kwamitin MDD mai mambobi 15, ta ayyana kasar Libya da cewar, tamkar wata mafaka ce ta 'yan ta'adda a yankin Sahel, kuma yaduwar makamai a tsakanin jama'a ne ya haddasa matsalar ta yi kamari.(Ahmad Fagam)