Wani jami'in kasar Somaliya ya bayyana a jiya Talata 6 ga wata cewa, an kaddamar da wani harin nakiya a wata kasuwa dake birnin Mogadishu, hedkwatar kasar Somaliya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 3.
Ban da wannan kuma, an kai wani harin na igwa, a wani yanki dake dab da fadar shugaban kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula a kalla 4.
Kawo yanzu dai babu wani mutum ko kungiya da ta sanar da daukar alhakin kaddamar da harin, ko da yake kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta al-Shabaab ta sha kai makamantan wadannan hare hare a sassan kasar. (Amina)