Mohamed Iska Aflow, shi ne shugaban gudanarwar hukumar tattara bayanan sirri na shiyyar kudu maso yammacin kasar Somaliya, ya shedawa 'yan jaridu a Jumma'ar da ta gabata cewa, wadanda aka kama, sun hada da kwamandan kungiyar ta IS na shiyyoyin Bay da Bakool, da sauran masu taimaka masa.
An kama mutanen ne kwana guda bayan Amurka ta bayyana sunan Abdulkadir Mumin jagoran kungiyar IS a Somaliya, cikin jerin sunayen 'yan ta'adda a gabashin Afrika. (Ahmad Fagam)




