in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmai sun gudanar da bukukuwan babbar Sallah a Xi'an dake yammacin Sin
2016-09-13 13:50:15 cri

Jiya Litinin ta kasance babbar sallah, saboda muhimmancin wannan rana, musulmai da yawa sun gudanar da bukukuwa a birnin Xi'an dake yammacin kasar Sin. A cibiyar birnin Xi'an akwai unguwar 'yan kabilar Hui, inda akwai wani babban masallaci mafi dadewa a tarihin birnin. A lokacin sallahr Lahiya, Musulmai da yawansu ya wuce dubu daya suna taruwa a masallacin domin yin addu'a. A sa'i daya kuma, cikin ungwannin dake dab da masallacin, wasu kantuna masu sayar da nama, da abinci, da kayayyakin da musulmai su kan yi amfani da su, dukkansu suna samun baki sosai.

Wakilinmu ya iske wani kanti wanda tuni aka yi cinikin hulunan da ake sanyawa a yayin bikin addu'ar har fiye da dari, yayin da ya rage sa'a guda gabanin fara bikin a masallacin. Cikin wadanda suka sayi hular, akwai mazauna wuri, gami da Musulmai da suka zo daga wurare masu nisa. Amir, wani dalibi dan kasar Pakistan dake karatu a birnin Beijing.

"Sunana Amir, na yi shekara daya da rabi a nan kasar Sin. Kwanaki 2 da suka wuce na bar Beijing na zo nan Xi'an. A yau mun zo nan wajen ne, domin murnar sallahr Lahiya, wadda ta kasance wani babban biki mai cike da murna ga dukkan Musulmai na kasashe daban daban."

Chaudry, abokin karatun Amir ne wanda shi ma ya zo daga kasar Pakistan. Ya ce abubuwan da ya gani sun burge shi sosai, kuma yana murna matuka ganin yadda ya samu damar bikin babbar sallah tare da Musulmai Sinawa.

"Wannan ita ce babbar sallah ta farko da na yi a nan kasar Sin. Ina farin ciki kwarai da gaske. A nan wurin za ka ga akwai masallatai da yawa, da 'yan uwanmu Musulmi da yawa. Bayan mun yi addu'a a Masallaci, mun yi kallon bikin yanka dabbobi. Yana da ban sha'awa sosai."

Shameel, wanda shi ma ya zo daga kasar Pakistan, wanda ya shafe shekaru 3 yana zaune a birnin Xi'an, don haka ya san al'adun Musulmai Sinawa sosai."Yadda ake bikin babbar sallah a nan ya sha bamban da yadda ake a kasarmu Pakistan. A nan a kan kai dukkan dabbobi zuwa masallaci domin a yanka su baki daya, ta wannan hanya ba za a sake bukatar neman wuraren yanka dabbobi masu zaman kansu ba. Wannan mataki ya sha bamban da tsarinmu sosai."

Birnin Xi'an ya yi suna wajen samar da nau'ikan abinci masu dadin ci. Kuma yawancin wuraren cin abinci na birnin suna wajen titin 'yan kabilar Hui, inda ake samun cunkuson mutane sosai a lokacin babbar sallah. Wakilinmu ya gamu da wasu 'yan matan kasashen waje a nan, wadanda suka gama biki a masallaci, suna tattaunawa kan inda za su tafi don cin abinci."Sunana Sojia, na zo daga kasar Somaliya. Ni daliba ce a jami'ar koyon fasahar kimiyyar lantarki ta birnin Xi'an. Yau ni da abokaina mun zo masallaci domin addu'a. Za ka ga wani yanayin biki a nan mai annashuwa da murna. Dazu nan muka gama bikin addu'a, muna neman wurin cin abinci."

Wata abokiyarta ita ma ta fadi cewa,

"Sunana Mia, ni 'yar kasar Yemen ce. Yau na zo masallaci addu'a, kuma ina farin ciki kwarai, ganin Musulmai Sinawa da yawa suna tare da mu wajen bikin babbar sallah. Sai dai ina begen iyalina a wannan lokacin biki."

Ban da Musulmai 'yan kasashen waje, su ma kansu Sinawa mabiya addinin Musulunci sun zo Xi'an daga wurare daban daban na kasar Sin, domin jin dadin yanayin bikin a wannan tsohon birni. Ma Dongyan, ta zo daga lardin Yunnan na kasar Sin, wadda ke ziyarar aiki a Xi'an. Ita ma ta je masallacin domin gudanar da bikin addu'ar babbar sallah, daga bisani ta je unguwar dake dab da masallacin don cin abinci. Ta ce,

"Muna murna kwarai, domin mun zo a daidai lokacin babbar sallah. Yanayin yadda ake sallah ya burge ni, kuma ana samar da abinci masu dadin ci sosai."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China