in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnonin Najeriya na ziyarar fadada hadin gwiwa da kasar Sin
2016-08-12 13:58:00 cri

Yanzu haka wasu daga gwamnonin Najeriya na ci gaba da ziyarar aiki a nan birnin Beijing na kasar Sin, a wani mataki na cimma nasarar aiwatar da yarjeniyoyin da Najeriyar ta kulla da kasar Sin.

Kungiyar kulla kawance tsakanin al'ummun kasar Sin da na sauran sassan duniya ta nan kasar Sin ce ta shirya wannan ziyara, inda kuma tuni gwamnonin suka fara ganawa da wasu daga kamfanonin kasar Sin masu sha'awar zuba jari a Najeriya.

Yayin zantawar wakilin mu da gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, gwamnan ya bayyana irin gajiyar da jahohin Najeriya ke fatan ci daga ziyarar ta wannan karo, tare da irin darussan da Najeriya ka iya koya daga ci gaban da kasar Sin ta samu.

A Yau Juma'a ne kuma tawagar gwamnonin ta ziyarci ofishin kamfanin gine gine na CRCC dake nan birnin Beijing, domin tattaunawa da jagororin sa, game da hanyoyin hadin gwiwa da ciyar da jahohin nasu gaba.

Da yake jawabi yayin ganawar, babban daraktan kamfani mai kula da harkokin kasa da kasa Mr. Liao Jun, ya ce kamfanin na CRCC ya dade yana gudanar da ayyuka a Najeriya, zai kuma duba yiwuwar gudanar da karin hadin gwiwa tsakanin sa da wasu jahohin kasar a fannin gina ababen more rayuwa, kamar hanyoyin mota, da layin dogo, da kuma fannin samar da wutar lantarki da dai sauran su.

Gwamnonin dai sun gabatar da sassa daban daban da suke fatan kamfanin zai hada kai da jahohin su domin cimma moriyar juna.

Tawagar gwamnonin karkashin jagorancin gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Abubakar Yari, ta kunshi gwamnonin Anambra, da Delta, da Jigawa da Oyo da Plateau da kuma wakilin gwamnan jihar Adamawa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China