in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta dauki matakai daban daban domin sauya salon bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu
2016-07-18 13:17:37 cri

A kwanan baya ne, aka shirya bikin baje koli da taron kara wa juna sani kan fasahohin bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu karo na 9 na kungiyar APEC a birnin Shenzhen da ke nan kasar Sin. Yawan kanana da matsakaitan masana'antun da ke kasar Sin ya kai kashi 99.7 cikin dari na jimillar masana'antun kasar baki daya, sabo da haka, suna da muhimmanci matuka ga tattalin arzikin kasar Sin. Kanana da matsakaitan masana'antu su da yawa a nan kasar Sin. Mr. Ma Xianghui, mataimakin direktan hukumar kula da kanana da matsakaitan masana'antu a ma'aikatar manasana'antu da sadarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "kanana da matsakaitan masana'antu suna da muhimmanci sosai wajen kirkiro sabbin fasahohi, da samar da guraben aikin yi. Yawan harajin da suke samarwa ya kai kashi 50 cikin dari na jimillar harajin da gwamnati ta samu, sannan yawan guraben aikin yi da suka samar ya kai kashi 80 cikin kashi dari. A saboda haka ne muka ce, suna da muhimmanci matuka ga tattalin arzikin kasar Sin."

Amma a yanzu, kanana da matsakaitan masana'antu na kasar Sin suna fama da kalubaloli iri iri. Alal misali, suna shan wahalar samun jarin da suke bukata, suna kashe kudade da yawa wajen hayar filin da za su kafa masana'antu, sannan suna shan wahalar daukar ma'aikatan da za su yi musu aiki da dai makamantansu. A yayin bikin baje koli da taron kara wa juna sani kan fasahohin bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu karo na 9 na kungiyar APEC da ya gudana a birnin Shenzhen, Mr. Feng Fei, mataimakin ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin ya bayyana cewa, za a dauki matakai iri daban daban don taimakawa kanana da matsakaitan masana'antu. Feng Fei ya ce, "Za a rage matakan yau da kullum na neman izinin kafawa da kuma bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu, sannan za a tanadar musu kasafin kudi da kuma rage harajin da suke biya, musamman wasu kanana masana'antu, za kuma a rage, har ma soke harajin da suka biya wajen yin nazari, da yin musaya da kuma kirkiro sabbin fasahohi."

Kanana da matsakaitan masana'antu suna shan wahala sosai wajen samun rancen kudi daga bankuna sabo da ba su girma ba, ana da shakku a kansu, kuma ba su da isassun dukiya ko kadarori. Feng Fei ya kara da cewa, dole ne a kyautata yanayin hada-hadar kudi, ta yadda za a iya rage wahalhalun da kanana da matsakaitan masana'antu ke fuskanta wajen samun jari, kuma ya kamata a rage yawan kudin da kanana da matsakaitan masana'antu suke kashewa domin samun jari. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin kafa asusun bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu, inda aka tanadi asusun RMB yuan biliyan 60 domin taimakawa sabbin kanana da matsakaitan masana'antu. Fei Fei ya ce, "Za a kirkiro sabbin fasahohin hada-hadar kudi domin tallafawa kanana da matsakaitan masana'antu. Sannan za a rage yawan kudin ruwa da kanana da matsakaitan masan'antu suke biya don biyan bukatun da ake da su a kasuwanni. Bugu da kari, za a rage yawan kudin ajiyar bankuna domin tallafawa kananan da matsakaitan masana'antu wadanda suke bukatar karin rancen kudi da kuma rage kudin da suke kashewa a lokacin da suke hada-hadar kudi."

Amma, daga karshe dai, Mr. Feng Fei ya kara da cewa, dole ne kanana da matsakaitan masana'antu su yi kwaskwarima kan kayayyakin da suke samar wa a kasuwanni domin biyan bukatun harkokin kasuwanni. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China