in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta bayar da sanarwa kan 'yancin da take da shi a yankin tekun kudancin kasar da kuma yankin baki daya
2016-07-12 19:18:11 cri

A kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi na nanata 'yancin da take da shi a yankin tekun kudancin kasar da kuma hakkinta a yankin, bisa aniyar inganta hadin kai da sauran kasashen dake yankin tekun kudancin kasar da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, yau Talata 12 ga wata, gwamnatin ta bayar da wata sanarwa, inda ta ce, tsibiran da ke tekun kudancin kasar Sin sun hada da tsibiran Dongsha, da na Xisha, da na Zhongsha, da kuma na Nansha. Al'ummar kasar Sin sun fara gudanar da ayyukansu a yankin yau kusan fiye da shekaru dubu biyu. kasar Sin ita ce kasa ta farko da ta gano tsibiran da kuma fadin tekun, sannan ta nada masu sunaye, ta kuma raya ayyuka a wurin. Haka kuma ita ce kasa ta farko da ta mallaki wurin cikin lumana ba tare da katsewa ba, hakan ya sa aka tabbatar da 'yancin kasar Sin a tekun kudancin kasar. Bayan da aka kawo karshen yakin duniya na biyu, kasar Sin ta maido da tsibiran tekun kudancin kasar daga hannun kasar Japan wadda ta mamaye su ba bisa doka ba a yayin da ta kaiwa wa kasar Sin hare-hare, daga nan ne Sin ta ci gaba da mallakar wurin. Tun bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, gwamnatin kasar Sin take tsayawa tsayin daka kan kiyaye 'yancinta a yankin tekun kudancin kasar.

Ikon mulkin kasar Sin da kuma hakkinta kan yankin tekun kudancin kasar sun hada da bangarori guda hudu, matsayin kasar Sin kan batun da kuma dokokin kasar da yarjejeniyar teku ta MDD da sauran dokokin kasa da kasa da abin ya shafa. Wadannan bangarori hudu su ne: Na daya, kasar Sin tana da 'yancin mallakar dukkan tsibiran dake yankin tekun kudancin kasar Sin, watau tsibiran Dongsha, tsibiran Xisha, tsibiran Zhongsha da kuma tsibiran Nansha. Na biyu, tsibiran dake yankin tekun kudancin kasar Sin sun hada da yankin tekun dake cikin tsibiran, da yankin teku dake karkashin mallakar tsibiran har ma da yankunan da ke makwabtaka da su. Na uku, tsiriban dake yankin tekun kudancin kasar Sin suna da yankin musamman na tattalin arziki da kuma bangaren da ke kan iyakar tsibiran da ya tafi har zuwa yankin teku. Na hudu shi ne, kasar Sin tana da 'yanci na tarihi kan yankin tekun kudancin kasar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, kasar Sin tana nuna kiyyaya ga wasu kasashen da suka mamaye wasu tsibiran dake yankin tsibiran Nansha na kasar Sin, haka kuma, wasu ayyukan da suka aikata a yankin tekun kudancin kasar Sin sun keta 'yancin kasar Sin kan wannan yanki. Don gane da wannan lamari, kasar Sin tana fatan yin shawarwari da kasashen da abin ya shafa, domin habaka wannan yankin cikin hadin gwiwa, ta yadda za a iya cimma moriyar juna da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki yadda ya kamata.

Bugu da kari, sanarwar ta ce, kasar Sin tana girmama da kuma amincewa da 'yancin kasashen duniya na zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin da kuma jiragen sama a kan yankin, haka kuma, tana son yin hadin gwiwa da kasashen dake kewayen yankin tekun kudancin kasar Sin da gamayyar kasa da kasa wajen kiyaye tsaron hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin tekun kudancin kasar Sin. (Kande/Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China