in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tekun kudancin kasar Sin ba ya nufi dukkan fadin tekun da ke kudancin kasar Sin, in ji wani masanin kasar Sin
2016-07-05 14:10:03 cri

A hakika dai, sau da dama kasashen Amurka da Japan da wasu kasashen Asiya sun sha yin amfani da "Layuka tara da aka shata kan iyakar tekun kudancin kasar Sin" wajen tsokanar kasar Sin. Haka kuma wasu mutane sun sha nuna shakku kan halalcin wadannan layuka tara a gun tarurukan kasa da kasa da ke da nasaba da batun tekun kudancin kasar Sin. Ko da yake an nuna shakkun ne domin takalar kasar Sin, amma mayar da martani kanta ba wani abu mai sarkakiya ba ne. Farfesa Feng Wei na sashen ilmin tarihi na jami'ar Fudan ta kasar Sin ya furta cewa, ya kamata a kira Layuka tara da suna "Layi mai siffar baka", wanda ya sheda 'yancin kasar Sin bisa tarihi a tekun da ke kudancin kasar, Feng Wei ya kara da cewa,

"An shata layin ne a shekarar 1947 domin raba iyaka da sauran kasashe. A wancan lokaci ma, lauyukan guda 11 ne. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, sai aka kira layin da suna 'layi mai siffar baka', sa'an nan aka cire layuka guda biyu da aka shata a kasar Vietnam, don haka yanzu a ke kiran layin da suna 'Layuka tara'. Idan muka dubi taswirar fadin tekun kasashen Amurka da Birtaniya a wancan lokaci, za mu ga cewa, kasar Sin ta mallaki wadannan wurare. A wannan karo, nufin kasar Philippines a kan batun shi ne, ba ta so a yanke hukunci kan wane tsibiri ko wadanne duwatsu, sai layi mai siffar baka da kasar Sin ke mallaka tun fil azal."

Batun shata iyakar kasar Sin a tekun da ke kudancin kasar, batu ne na dogon lokaci. Kuma an shata layuka tara ne bayan da kasar Sin ta karbi ikon mallakar tsibiran Xisha da Nansha daga hannun kasar Japan. Amma, wasu sun nuna shakkar cewa, a wancan lokaci, kasar Philippines ba ta samu 'yancin kanta ba, kasar Vietnam ita ma tana fama da yakin basasa, don haka ba su kula da batun shata kan iyakar su da kasar Sin ta yi ba. Game da wannan, farfesa Feng Wei na ganin cewa, irin wannan ra'ayi bai yi daidai ba. Ya ce,

"Ko sun kula ko ba su kula ba, wannan ba ya da nasaba da 'yancin kasar Sin na mallakar tekun kudancin kasar. Wani abu mai muhimmanci shi ne, kasar Sin ba ta da aniyar danne musu 'yanci a wannan fadin tekun. Don haka, ana iya gano cewa, gaskiya dai halin da wadannan kasashe ke ciki ba ya da alaka da 'yancin kasar Sin a fadin tekun da ke kudancinta ."

Kasar Philippines ta gabatar da kara don yanke hukunci kan batun tekun kudancin kasar Sin, inda ta mai da hankali kan yanke hukunci kan halalcin "Layuka tara" da kasar Sin ta shata a tekun da ke kudancin kasar. Dalilin da ya sa kasashen Philippines da Vietnam da Amurka da kuma Japan ke iya amfani da wannan batu wajen tsokanar kasar Sin shi ne sabo da har yanzu kasar Sin ba ta sanar da 'yancinta game da wadannan Layuka tara, da kuma bayyana abubuwa da Layukan ke nufi. Don me gwamnatin kasar Sin ba ta yi bayani takamaimai kan Layukan ba? Game da wannan, farfesa Feng Wei ya nuna cewa, sabo da ko da yaushe kasar Sin ta nuna sahihancinta don kaucewa duk wani rikici don gudun tsanantarsa. Feng yana mai cewa,

"A wani bangare, kasar Sin ta jaddada ikonta na mallakar tekun kudancin kasar, da daukar ra'ayin kaucewa rikici da raya tekun tare. Amma a wani bangare na daban, ko da yaushe kasar Sin ta ba musunta kasancewar sabani kan ikon mallakar tekun da ke kudancin kasar. Domin magance tsanantar rikicin, kasar Sin ba ta shata layin iyakar kasa a wasu sassan fadin tekun ba. Fadin tekun da ke kudancin kasar Sin ya kai muraba'in kilomita miliyan uku da dubu 650, amma fadin tekun da kasar Sin ke batun 'yancin mallakarsa ya kai muraba'in kilomita miliyan biyu da dubu 100. Don haka, batun tekun kudancin kasar Sin ba ya nufi dukkan fadin tekun da ke kudancin kasar. Amma da ganga kasashen yammacin duniya suka juya jimlolin biyu domin ta da hargitsi, da nufin sheda cewar, wai kasar Sin tana kwadayin mallakar dukkan fadin tekun ne. Hakika wannan makarkashiya ce kawai suka shirya."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China