in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukuncin da za a yanke kan batun tekun kudancin Sin zai kasance tamkar takardar kunshe tsire, in ji Dai Bingguo
2016-07-06 14:56:12 cri

A jiya Talata, aka shirya wani taron tattaunawa kan batun tekun kudancin Sin a birnin Washington DC, hedkwatar kasar Amurka, inda aka tattauna kan batun "tekun kudancin Sin ta mahangar kasar Sin da ta Amurka" da "gano sabani da makomar yankunan tekun kudancin Sin daga bangarori daban daban" da "tunani da shawarar warware batun tekun kudancin Sin bisa hakikanin halin da ake ciki". A yayin bikin kaddamar da taron, Mr. Dai Bingguo, tsohon mamba a majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, hukuncin da za a yanke kan batun tekun kudancin Sin zai kasance tamkar wata takardar kunshe tsire ce kawai. Ko shakka babu, kasar Sin za ta rike cikakken ikon mulkin dukkan yankunanta kamar yadda ya kamata, kuma ba za ta amince da kowane irin shirin daidaita batun da bangare na uku zai fitar ba. Yanzu ga rahoton da abokin aikinmu Sanusi ya hada mana.

A yayin bikin kaddamar da taron, Mr. Dai Bingguo ya gabatar da wani jawabi, inda ya nuna cewa, a 'yan watannin da suka gabata, yankin tekun kudancin Sin inda ake cikin kwanciyar hankali a da, ya zama wuri maras kwanciyar hankali yanzu, har ma ya zama wurin dake jawo hankulan duk duniya. Mr. Dai ya ce, "A ganina, yawancin rahotonni da sharhohin da ake bayarwa game da batun tekun kudancin Sin sun nuna wani sashe ne kawai game da batun, ba su nuna hakikanin dukkan abubuwa game da wannan batun. Ina tsammanin cewa, a lokacin da ake nazarin wani batun dake jawo hankulan duniya, dole ne a yi shi bisa hakikanin halin da ake ciki, kuma a yi la'akari da tarihin batun da abubuwan dake bayan batun. Bugu da kari, dole ne a sa ido kan yadda bangarorin da batun ya shafa suke yin mu'amala da juna a kokarin sanin ainihin batun, da kuma samun cikakken sakamako."

Mr. Dai Bingguo ya nuna cewa, takardun tarihi dake hannun kasar Sin da na sauran kasashen duniya dukkansu sun shaida cewa, jama'ar kasar Sin sun riga jama'ar sauran kasashen duniya gano tsibiran, da kuma raya tsibiran dake yankin tekun kudancin Sin. Bugu da kari, gwamnatin kasar Sin ce ta riga gwamnatocin sauran kasashen duniya tafiyar da ikon mulkin wadannan tsibirai.

Dai Bingguo ya kara da cewa, a cikin shekaru masu tarin yawa da suka gabata, halin da ake ciki a yankin tekun kudancin Sin yana cikin kwanciyar hankali, yankunan dake kudu maso gabashin Asiya ma sun samu bunkasa cikin sauri. Wannan gagarumar gudumma ce da kasar Sin da sauran kasashen dake yankin suke bayarwa ga duniya baki daya. Ko da yake yanzu an samu wasu matsaloli wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, amma kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen bin manufar daidaita batun cikin lumana ta hanyar yin shawarwari, kasar Sin ba ta canja wannan matsayin da take dauka ba.

"Kowa ya sani, gwamnatin kasar Sin ce ta riga sauran kasashe fitar da manufar 'ajiye rigingimu domin bunkasa wurin cikin hadin gwiwa' domin kokarin kawar da rigingimu cikin lumana ta hanyar yin shawarwari da tattaunawa, ta yadda za su iya bunkasa da kuma cin moriya tare a yankin. Bugu da kari, tana kokarin tabbatar da zaman lafiya da yin zirga-zirga a yankin cikin 'yanci. Wannan ne babbar manufar da kasar Sin take bi wajen daidaita batun tekun kudancin Sin, kuma alkawari ne da ta yi wa duniya."

Dai Bingguo ya jaddada cewa, kasar Phillippines ita kadai ce ta gabatar da kara kan batun tekun kudancin Sin ba ma kawai ta sabawa matakan da bangarorin da batun tekun kudancin Sin ke shafa za su dauka ba, har ma ya sabawa jerin yarjejeniyoyin da ta kulla da bangaren Sin da ka'idojin "Yarjejeniyar dake shafar harkokin teku ta MDD", sakamakon haka, tun daga farko zuwa karshe, irin wannan matakin da kasar Phillippines ta dauka mataki ne dake keta dokoki. Hukuncin da za a yanke zai kasance tamkar wata takardan kunshe tsire ce kawai. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China