in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AMISOM ta karyata zarge-zargen sata a Somaliya
2016-08-31 11:12:05 cri

A jiya Talata ne rundunar wanzar da zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afirka wato AU wao AMISOM ta tura a kasar Somaliya ta musunta wasu labarun da ke cewa, jami'an tsaron wurin sun cafke wasu sojoji biyu na rundunar da ake tuhumarsu da sayar da kayayyakin soja ba bisa ka'ida ba a kasar Somaliya da ke yankin gabashin Afrika.

A wata sanarwar da rundunar AMISOM ta fitar, ta nanata cewa, babu wani sojin AMISOM da hukumar leken asirin kasar ta cafke a ranar Litinin a birnin Mogadishu bisa dalilin sayar da kayayyakin soja ba bisa ka'ida ba.

Rundunar ta ce, labarun ba su da tushe. A shirye take domin kawo cikakkun shaidu game da wannan batu.

Wasu kafofin watsa labarun kasar sun ruwaito a ranar Litinin cewa, 'yan sanda sun cafke wasu sojoji biyu, kuma jami'an leken asirin Somaliya sun tsare motarsu a Mogadishu inda ake tuhumar su da sayar da kayayyakin soja da kuma man fetur ba bisa doka ba.

A cewar rahotonnin, 'yan sanda sun jima suna bincike kan wannan batu, bayan gano wasu kayayyakin AMISOM a hannun al'umma.

Rundunar AMISOM dai na kushe da sojojin wanzar da lafiya fiye da 22000 dake taimakawa wajen maido da zaman lafiya da zaman karko a Somaliya.(Laouali Souleymane).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China