in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a harin bam din Somaliya ya karu zuwa 22
2016-08-31 10:03:19 cri

Rahotanni daga kasar Somaliya sun nuna cewa, yawan mutanen da suka mutu a sanadiyar harin bam din da aka kai a cikin wata mota kan otel din SYL da ke kusa da fadar shugaban kasar a Mogadishu, babban birnin kasar ya karu zuwa 22 yayin wasu 30 kuma suka jikkata.

Shugaban sashen kula da motocin daukar marasa lafiya na birnin Amiin, Abdulkadir Andirahan Haji Aden ya ce, akwai mata guda biyar a cikin jami'an tsaron da harin ya rutsa da su. Kana bayan harin an kuma kwashe gawawwakin mutane 22 baya ga wasu mutane 30 da suka ji rauni ciki har da minista guda, da 'yan majalisun dokoki da dama da kuma 'yan jaridu biyu.

Wani jam'in 'yan sanda da lamarin ya faru a kan idonsa mai suna Mahad Farah ya shaida wa kamfanin dillancin larabai na Xinhua na kasar Sin cewa, fashewar ta faru ne, 'yan mitoci kadan daga mashigar otel din na SYL, lokacin da masu gadi suka bude wa wata karamar mota wuta da suke zargin matukinta yana kokarin kaddamar da hari.

Daga bisani dai kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari. A shekarar 2011 ne dai aka fatattaki kungiyar daga Mogadishu, amma har yanzu tana haifar da barazana ga gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan MDD, inda take yawan kaddamar da hare-hare a birnin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China