A nasa bangaren, Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, an samu muhimmin sauyi dangane da halin da ake ciki a kasar Sham. A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin na da ra'ayoyi uku kan batun Sham, na farko dai, ya kamata kasashen duniya su hada karfi don yakar ta'addanci. Bangaren Sin na goyon bayan matakan yakar ta'addanci da za a dauka muddin da aka samu amincewar kasar da abin ya shafa bisa dokokin kasa da kasa, sannan yana fatan bangarori daban daban su kara yin mu'amala da daidaitawa tare da hada kai da juna. Sannan, ya kamata a hanzarta daukar matakan warware batun a siyasance. Kasar Sin na maraba da kasashen duniya su kaddamar da sabbin matakan shiga tsakani ta yadda za a daidaita batun kasar ta Sham a siyasance. Bugu da kari, wajibi ne a sassauta rikicin jin kai da al'ummar kasar ke fuskanta. Dimbin 'yan gudun hijira daga yankin Gabas ta tsakiya na kawo cikas ga kwanciyar hankalin yankin da sauran kasashe makwabta. Sabili da haka, ya kamata bangarori daban daban su kara daukar matakan sassauta rikicin jin kai a kasar. Kasar Sin za ta ci gaba da ba da tallafi bisa karfinta.
Mr. Shaaban ya nuna cewa, bangaren Sham na goyon bayan dukkan kokarin daidaita batun Sham a siyasance, kuma yana yabawa matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun Sham. Mr. Shaaban yana maraba da kasar Sin ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kawo karshen matsalar kasar ta Sham. (Sanusi Chen)