Yau Talata 29 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya sanar da cewa gwamnatin kasar Sin, ta nada mista Xie Xiaoyan a matsayin manzon musamman mai kula da batun Sham.
A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Hong Lei ya ce, yanzu an shiga muhimmin lokaci na daidaita batun Sham. Dalilin da ya sa kasar Sin ta nada wannan manzon musamman shi ne domin ganin an kara nuna hikimar kasar Sin, da fito da dabarar kasar Sin wajen shiga tsakani a batun na Sham, kana a inganta tuntubar juna a tsakanin sassa daban daban masu ruwa da tsaki, ta yadda Sin za ta kara taka rawa wajen warware batun a karshe yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)