Kwanan baya ne, kasashen Rasha, da Amurka, da babban sakataren MDD suka bayyana ra'ayoyinsu tare da gabatar da shawarwari kan yadda za a kai ga warware batun kasar Sham.
Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana yau Laraba a nan Beijing cewa, kasar Sin ta lura da shawarwarin da sassa daban daban suka gabatar game da warware batun Sham.
Kasar Sin tana goyon bayan duk wata hanyar da za a bi wajen warware batun a siyasance. Kana, kasar Sin na ganin cewa, wajibi ne a tukari hanyar warware batun a siyasance, a tabbatar da ganin cewa, jama'ar Sham sun zabi makomar kasarsu da kansu, a gudanar da shirin shimfida tsarin siyasa, wanda zai rungumi sassa daban daban, a kuma gaggauta shirya tattaunawar siyasa cikin adalci, wadda za ta bude kofa ga kowa da kowa. Har wa yau wajibi ne a tsaya tsayin daka wajen samun sulhuntawa tsakanin al'ummar kasar da kuma hada kan kasar ta Sham, tare kuma da ci gaba da kara samar da agajin jin kai a Sham da kuma kasashen da ke makwabtaka da ita. Haka zalika, dole ne a yi la'akari da yadda ake yaki da ta'addanci a kasar Sham yayin da ake kokarin warware batun Sham. (Tasallah Yuan)