Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei wanda ya bayyana hakan yau a nan birnin Beijing ya ce, kasar Sin na kira da a yi amfani da matakan siyasa da za su dace da bukatun sassan da batun ya shafa wajen warware rikicin kasar.
Hong Lei ya ce kasar Sin tana maraba da yadda sassan kasar ta Syria suka martaba yarjejeniyar tsagaita bude wutan da aka cimma. Sannan ta bukaci dukkan bangarorin kasar da su cimma daidaito game da bambance-bambancen da ke tsakanisu.
Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da sauran kasashen duniya wajen taka rawar da ta dace a kokarin da ake na warware rikicin siyasar kasar ta Syria.
A jiya ne babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, yarjejeniyar tsagaita bude da aka cimma tsakanin gwamnatin Syria da dakarun 'yan adawar kasar tana aiki. (Ibrahim Yaya)