in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwajin makaman nukiliya zai lalata yanayin zaman karko a zirin Koriya
2016-09-11 13:29:31 cri
Jiya Asabar, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Yesui ya gana da jakadan kasar Koriya ta Arewa dake nan kasar Sin Chi Jae Ryong, domin nuna matsayin kasar Sin kan gwajin makaman nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ta sake yi a kasar kwanan baya.

A yayin ganawar tasu, Zhang Yesui ya bayyana cewa, dangane da batutuwan dake shafar zirin Koriya, kullm kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, da kiyaye zaman lafiya da zaman karko a zirin, da kuma warware sabani ta hanyar yin shawarwari.

Amma kasar Koriya ta Arewa tana cigaba da raya makaman nukiliya, da kuma yin gwajin makaman nukiliyarta, lamarin da ya rusa fatan gamayyar kasa da kasa, sannan ya kuma lalata yanayin zaman lafiya da zaman karko a zirin Koriya. Shi ya sa, kasar Sin ta bukaci kasar Koriya ta Arewa da kada ta cigaba da daukar matakan da za su haddasa tashe-tashen hankula a wannan yanki, da kuma nemo hanyar kawar da makaman nukiliya cikin sauri. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China