in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron tunawa da ranar yaki da Amurka a Koriya ta Arewa
2016-06-26 14:47:59 cri
A jiya Asabar, mazauna birnin Pyongyang, babban birnin kasar Koriya ta arewa sama da dubu 100 sun yi gangami da zanga zanga a filin Kim Il-sung domin tunawa da ranar yaki da Amurka.

A gun taron, shugaban kwamitin jama'ar birnin Pyongyang, Cha Hui-rim ya bayyana cewa, yau da shekaru 66 da suka wuce, sojojin Amurka sun kai hari kan kasar Koriya ta Arewa, wanda ya haifar da manyan illoli ga rayuwar jama'ar kasar. A halin yanzu kuma, Amurka tana yunkurin keta ikon 'yanci da na rayuwar Koriya ta Arewa, tare da tsananta yanayin da ake ciki a zirin Koriyar. Dadin dadawa, Amurka ta yi atisayen soja tare da kasar Koriya ta Kudu har sau da dama, hakan ya kara tsananta yanayin zirin Koriya. Cha Hui-rim ya yi Allah wadai da Amurka da ta yi fatali da bukatar Koriya ta Arewa ta gabatar game da daina gudanar da atisayen soja da Koriya ta Kudu, kuma ya zargi Koriya ta Kudu da rashin amincewa da kokarin Koriya ta Arewa na yin shawarwari tsakanin bangarorin biyu, tare da kara yin barazana ga Koriya ta Arewa a fannin siyasa da aikin soja.

Wakilai daga bangarorin ma'aikata da manoma da dalibai sun gabatar da jawabai a wajen taron. Daga bisani, an yi gagarumar zanga zangar yaki da Amurka a filin Kim Il-sung. A ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 1950, yakin zirin Koriya ya barke. Kasar Koriya ta Arewa ta mayar da wannan rana a matsayin ranar yaki da Amurka.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China