in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na M.D.D. ya yi Allah-wadai da harbar makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ta yi
2016-04-25 09:14:27 cri
A jiya Lahadi ne kwamitin sulhu na M.D.D. ya ba da wata sanarwa, wadda ke Allah-wadai da harbar makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ta yi a ranar 23 ga wata. Sanarwar ta ce matakin da Koriya ta Arewa ta dauka ya saba wa kudurorin kwamitin sulhu na M.D.D, kana kwamitin sulhun M.D.Dr na dukufa ka'in da na'in, wajen warware yanayin da ake ciki ta hanyar diplomasiyya cikin lumana.

Kwamitin sulhun ya kuma bukaci sauran mambobin kwamitinsa da su cimma matsaya guda, wajen warware wannan kalubale cikin lumana kuma daga duk fannoni. Kwamitin sulhu na M.D.D. ya ce, zai ci gaba da la'akari da yanayin da ake ciki a kasar, tare da daukar karin matakai.

A daya hannun ita ma gwamnatin Koriya ta Kudu ta yi Allah-wadai da matakin da Koriya ta Arewa ta dauka na harba makamai masu linzami, kuma a cewarta, za ta yi hadin gwiwa da kasashen duniya, don daukar matakai na hakika.

Koriya ta Arewa dai ta gudanar da taron kwamitin tsakiyar kasar, don bikin murnar cika shekaru 84 da kafa sojojin jama'ar Koriya ta Arewa. A yayin taron ne kuma babban hafsan-hafsoshin sojojin jama'ar Koriya ta Arewa Ri Myong Su, ya yi kashedi ga kasashen Koriya ta Kudu da Amurka da kada su kalubalanci shugaban kasar sa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China