in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya la'anci Koriya ta Arewa kan harba makamai masu linzami
2016-06-02 13:09:17 cri
A jiya Laraba ne kwamitin sulhun MDD ya bayar da sanarwa ta kafofin watsa labaru, inda ya yi alla wadai da babbar murya kan yadda Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami da ba su yi nasara ba har sau uku, ya ce, hakan yin kunnen uwar shegu ne da sanarwar da kwamitin sulhu ya yi. Saboda haka, kwamitin sulhu ya yi kira ga kasashe mambobin MDD da su kara kokari don tabbatar da matakan da za a dauka kan Koriya ta Arewa bisa kudurin da aka tsaida, ya kuma ba da umurni ga kwamitin kakaba takunkumi da ya gaggauta aiwatar da kudurin.

Kwamitin sulhu ya kara bayyana bakin cikinsa saboda bambancin da ya kunno kai tsakanin mambobin kwamitin, saboda yanzu haka 'yan kasar Koriya ta Arewa na cikin wani hali, amma gwamnatin kasar ta yi amfani da albarkatun kasar domin kera makamai masu linzami.

A sa'i daya kuma, kwamitin sulhu ya nuna damuwa sosai kan jerin harba makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ta harba, bayan wadanda ta yi a ranar 15 da ranar 23 ga watan Aflilu.

Kwamitin sulhu ya sake nanata cewa, kamata ya yi Koriya ta Arewa ta dakatar da daukar matakan da za su saba wa kudurorin kwamitin sulhu, ciki har da yin gwajin makaman nukiliya, tare kuma da daukar nauyinta bisa kudurorin.

Baya ga haka, kwamitin sulhu ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya, da yankin arewa maso gabashin Asiya, ya kuma bayyana cewa, zai yi kokarin warware matsalolin da ake fuskanta a yanzu a siyasance ta hanyar lumana da diplomasiya, kana yana maraba da kasashe mambobinsa da sauran kasashe da su bullo da wani shirin warware matsaloli cikin lumana a dukkan fannoni.

Kwamitin sulhun kuma zai ci gaba da lura da halin da yankin ke ciki, kuma mai yiwuwa ne zai dauki matakai masu tsanani idan bukatar hakan ta taso. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China