in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya kalubalanci Koriya ta Arewa da ta girmama kudurin kwamitin
2016-06-24 13:10:28 cri
Kwamitin sulhun MDD ya bayar da wata sanarwa a jiya Alhamis 23 ga wata, inda ya yi Allah wadai da kasar Koriya ta Arewa kan yadda ta sake gwajin makamai masu linzami, tare da kalubalantarta da ta girmama kudurin kwamitin sulhun da abin ya shafa daga dukkan fannoni, da dakatar da sake irin wannan gwaji. Sanarwar ta kara da cewa, Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamai masu linzami sau da dama, matakin da ya sabawa kudurin da kwamitin sulhun ya tsaida, kuma kwamitin ya sake jaddada cewa, dole ne Koriya ta Arewa ta daina gwajin nukiliya, tare da kalubalantarta da ta girmama kudurin kwamitin sulhun daga dukkan fannoni. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China