Jiya Talata 9 ga wata ne, aka kaddamar da taron dandalin tattaunawar diflomasiyya taskanin al'ummar Sin da Afirka a Dar es Salaam, hedkwatar mulkin kasar Tanzaniya, wanda kungiyar kula da harkokin diplomasiyya a tsakanin al'ummar kasa da kasa ta kasar Sin da kuma gidan rediyon kasar Sin CRI suka shirya cikin hadin gwiwa. Inda mahalarta taron suka tattauna sosai a karkashin taken "hadin kai don samun nasara tare, da bunkasuwa gaba daya, a kokarin ciyar da dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka zuwa gaba daga dukkan fannoni".(Kande Gao)