A ranar Litinin, RPDC ta harba makaman roka guda uku a yankin ruwan tekun dake bakin gabarta. Wadannan gwaje gwajen makamai sun kasance wani babban laifi da Koriya ta Arewa ta aikata da suka sabawa kudurorin kwamitin sulhu, in ji mambobin kasashe goma sha biyar na kwamitin a cikin wata sanarwa.
A cikin sanarwar, kwamitin sulhu ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Koriya musamman ma shiyyar arewa maso gabashin Asiya, tare da kuma bayyana niyyarsa na bullo wata hanyar neman sulhu cin zaman lafiya, diflomasiyya da siyasa kan wannan matsala.
Mambobin kwamitin sulhu sun cimma ra'ayin ci gaba da sanya ido kan wannan matsala yadda ya kamata, kuma za su dauki sabbin matakai masu muhimmanci, kamar yadda niyyar kwamitin sulhu ta nuna a baya bayan nan, in ji sanarwar. (Maman Ada)