in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaben maye gurbin Ban Ki-moon: Kwamitin sulhu zai gudanar da wani sabon zabe a ranar 9 ga watan Satumba
2016-09-02 10:50:32 cri
Kwamitin sulhu na MDD zai gudanar a karo na hudu da wani sabon zabe a ranar 9 ga watan Satumba kan jerin 'yan takara guda goma domin neman maye gurbin mista Ban Ki-moon kan kujerar sakatare janar na MDD a ranar daya ga watan Janairun shekarar 2017, in ji shugaban kwamitin, jakadan kasar New Zealand, mista Gerard van Bohemen a ranar Alhamis.

Wani karin zabe zai gudana a ranar 26 ga watan Satumba, in ji jami'in. Amma duk da haka, mista Bohemen ya tabbatar cewa zai mika nauyin shirya zaben sirrin ga kasar Rasha ganin cewa wata 'yar kasar New Zealand, wato tsofuwar faraministar Helen Clark, tana cikin 'yan takarar guda goma.

Bayan kebabbun shawarwari na ranar alhamis da yamma, dukkan mambobin kwamitin sulhu sun amince da shirya idan akwai bukata da wani sabon zabe a farkon makon watan Oktoba.

A yayin zabe zagaye na uku, tsohon faraministan Portugal Antonio Guterres ya samu goyon baya a ranar Litinin daga kasashe goma sha daya cikin kasashe mambobi goma sha biyar, sauran kasashe uku sun nuna rashin gamsuwa da takararsa, yayin da kasar guda ta ce ba ta da wani ra'ayi. Haka kuma shiga gaban ministan harkokin wajen kasar Slovaque, mista Miroslav Lajacak wanda ya samu goyon bayan kasashe mambobi 9. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China