UNISDR ta jaddada cewa dandalin, da zai gudana a cikin watan Nuwamba, zai yi nazari kan matsaloli na yanzu da sauyin yanayi mafi tsanani ya janyo, da suka tura mutane miliyan 60 na yankin cikin bukata.
Amjad Abbashar, darektan cibiyar UNISDR shiyyar Afrika, ya bayyana cewa dandalin ya zo daidai lokacin da ake so, domin gwamnatoci da dama, da kungiyoyi na MDD da ma kungiyoyi masu zaman kansu (ONG) na yaki da mugun sakamakon bala'in El-Nino, da ya zo da karfi sosai a wannan shekara.
Baya ga haka, sauyin yanayi na kasancewa wani babban bala'i ga yawancin kasashe, in ji mista Abbashar a cikin wata sanarwa a birnin Nairobi na kasar Kenya.
Wannan dandalin zai zama wani muhimmin mataki wajen aiwatar da tsarin aiki na Sendai a kasar Afrika ta Kudu bisa ga bude hanyar wani salon bunkasuwa da zuba jari dake la'akari da haduran sauyin yanayi da bala'u daga indallahi da kuma gina daga karshe wani tsarin kariya da juriya ga bala'u, in ji mista Rhoda Peace Tumusiime, kwamishinan kungiyar tarayyar Afrika dake kula da tattalin arzikin karkara da noma.
Haka kuma, taron zai taimaka wajen bullo da wani matsayin Afrika da jadawalin aiki domin aiwatar da takardar aikin da aka cimma a Sendai. (Maman Ada)