A cewar hukumar ta WFP, sakamakon rashin tabbas wajen samun kudaden gudanar da shirin bayar da abinci a makarantun, yanzu haka, sama da yara 'yan makaranta dubu 500 a kasashen Kamaru, Mali, Mauritania da kuma Nijer za su fara zuwa makarantu ba tare da samun abinci ba, tun daga wata mai kamawa.
Ya zuwa karshen shekarar 2016, za'a janye tallafin ba da abinci ga yara 700,000 a kasashe 11.
Daraktan shirin WFP na shiyyar yammacin Afrika Abdou Dieng, ya fada cewar, za'a janye bada tallafin abincin ga kananan yaran ne a mafi yawancin kasashen yammaci da tsakiyar Afrika a daidai lokacin da ake fuskantar barazanar yunwa da karancin abinci mai gina jiki a kasashen.
A halin yanzu, hukumar tana neman agajin dala miliyan 48, domin ci gaba da gudanar da shirin ba da abincin ga yara 'yan makaranta a kasashen. (Ahmad Fagam)