A yayin wani taron manema labaru da aka shirya, Mr. Mistura ya ce, an tabbatar da wannan shiri ne, a yayin taron da bangarori uku na wakilan MDD, da kasashen Amurka da Rasha suka halarta kan batun na Sham, amma har yanzu ba a tabbatar da hakikanan matakan aiwatar da wannan shiri ba tukuna.
Bisa kudurin da aka tsaida a yayin taron kwamitin sulhu na MDD, an ce, ya kamata bangarori daban daban na Sham masu adawa da juna, su tabbatar da ka'idojin siyasa na wucin gadi, domin kokarin daddale wata yarjejeniya tsakaninsu, sai dai bisa halin da ake ciki yanzu, ba za a iya cimma wannan buri ba.
Mr. Mistura ya taba bayyana cewa, ya kamata a kaddamar da sabon zagaye na yin shawarwarin kawo zaman lafiya a lokacin da ya dace, ta yadda za a iya samun matakan kawo zaman lafiya na a zo a gani, wato a iya kawo karshen rikice-rikice a kasar Sham, da kuma kaddamar da shirin siyasa na wucin gadi wanda kowane bangaren siyasa na kasar ta Sham zai amince da shi. (Sanusi Chen)