in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan za a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma game da kasar Syria
2016-02-13 12:21:31 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira da a gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma game da kasar Syria, yayin taron birnin Munich da ya gabata a ranar Alhamis.

Mr. Wang ya ce an cimma gagarumar nasara wajen amincewa da wasu muhimman batutuwa a zaman taron, don haka ya wajaba dukkanin bangarorin da batun ya shafa, su hanzarta aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyin yadda ya kamata.

Da yake karin haske game da sakamakon taron na Munich a jiya Jumma'a, Mr. Wang ya ce wakilai 17 daga bangarorin kasa da kasa dake goyon bayan warware rikicin kasar ta Syria, sun cimma matsaya kan wasu matakai guda 3, wadanda suka hada da amincewa da matakan shigar da agajin jin kai ga masu bukata cikin kasar ta Syria. Sai kuma batun dakatar da kaddamar da hare hare da ake fatan aiwatarwa cikin mako guda, wanda kuma wani kwamitin aiwatarwa da Amurka da Rasha za su jagoranta, zai fidda tsare-tsaren gudanar da su. Kaza lika an amince da sake bude tattaunawar birnin Geneva ba tare da bata lokaci ba.

Mr. Wang ya sake jaddada bukatar ganin an cimma nasarar da aka sanya gaba, kamar dai yadda kasar Sin ta sha nuna goyon bayanta, ga daukar matakan wanzar da zaman lafita a kasar ta Syria. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China