Kwararrun sun bayyana hakan ne yayin da suke tattaunawa a dandalin samar da abinci a Afirka karo 6 da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya. Suna masu cewa, daukar matakan ya dogara ne ga masu ruwa da tsaki ta yadda za su inganta hanyoyi samun bayanai game da ayyukan gona da kuma kasuwanni.
Wani kwararre kan aikin gona na bankin raya Afirka Benedick Kanu, ya lura da cewa,fasahar sadarwa ta zamani za ta taimaka wajen zamanantar da tsare-tsaren samar da abinci a Afirka,a daidai lokacin da ake fuskantar matsalar canjin yanayi,tsoffin manufofi da wasu al'adu marasa kyau.(Ibrahim)