in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru a Afrika sun nemi a baiwa manoma tallafi
2016-06-15 10:51:26 cri
Mahalarta taron maku guda kan harkar noma karo na 7, sun bukaci a tallafawa kananan manoma a Afrika da kudade domin su samu damar noma kayan amfanin gona da za su sayar don samun kudin shiga da nufin samar da wadataccen abinci da kuma yakar talauci.

Kasar Rwanda ce ta karbi bakuncin taron na wannan karo na tsawon kwanaki 4, kuma sama da wakilai 1000 ne suka halarci taron daga kasashe dabam dabam na Afrika har ma da sauran sassa na duniya.

Taken taron na bana shi ne amfani da kimiyya don yin tasiri ga rayuwar dan adam.

Dr. Yemi Akinbamijo, shi ne babban daraktan dandalin bincike kan al'amurran noma na Afrika (FARA), ya ce mafi yawa daga manoman nahiyar Afrika na bukatar tallafin kudade domin samun damar bunkasa ayyukan su.

A cewar bankin raya ci gaba Afrika AfDB, a duk shekara sama da dalar Amurka biliyan 35 ne kasashen Afrika ke kashewa wajen sayo kayan abinci daga kasashen waje, sakamakon gazawa wajen noma wadataccen abinci a nahiyar.

Louis Butare, darakta janar na hukumar noma ta kasar Rwanda, ya ce sakamakon dogaro kwacokan da shuganbannin Afrika suke yi kan kungiyoyin ba da tallafi kan binciken al'amurran noma na kasashen duniya ne ya haddasa tabarbarewar al'amurran noma a nahiyar ta Afrika.

Butare, ya bukaci shugabannin Afrika da su canza salo wajen tunkarar al'amurran aikin gona, kuma su samar da isassun kudade a fannin domin samar da wadataccen abinci ga al'ummomin nahiyar.

Bugu da kari shugaban bankin raya ci gaban Afrika AfDB Dr. Akinwumi Adesina, ya sanar da cewa bankin ya ware dala biliyan 24 domin habaka aikin gona a Afrika cikin shekaru 10, da nufin samar da wadataccen abinci a nahiyar.

Taron na makon guda kan aikin gona wata babbar dama ce da za ta fahimtar da al'umma muhimmancin amfani da kimiyya da fasaha da kuma kere-kere wajen habaka aikin gona a nahiyar ta Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China