Bayanai na nuna cewa, alkawarin da bangrorin suka yi a yayin dandalin shirin samar da abinci Afirka karo na 6, an yi imanin cewa, shi ne kaso mafi yawa da aka taba kebewa bangaren aikin gona ya zuwa wannan lokaci. Kuma wannan shi ne matakin da ya shafi mafi yawan bangarori da aka taba dauka a kokarin da ake na samar da abinci a nahiyar.(Ibrahim)