in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afrika sun sha alwashin farfado da aikin gona
2016-09-08 10:55:51 cri

Shugabannin kasashe da gwamnatoci na Afrika da dama sun sha alwashin daukar matakan bunkasa aikin gona a fadin nahiyar.

Shugabannin sun bayyana hakan ne a yayin taron koli na Afrika game da aikin gona karo na 6 a Nairobin kasar Kenya, inda suka amince za su dauki matakan samar da kudade, da tsara dabaru, da yin amfani da fasahar zamani a matsayin hanyoyin da za su wadata nahiyar Afrika da abinci.

Shugaban kasar Kenyan Uhuru Kenyatta, a jawabinsa na bude taron, ya bayyana cewa, bunkasa aikin gona ita ce babbar hanyar da za ta habaka ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma a nahiyar Afrika.

Dubban wakilan gwamnati, da na kamfanoni, da masana, da kungiyoyin al'umma ne ke halartar taron kolin na Afrika game da aikin gona karo na 6, tsakanin ranakun 5 zuwa 9 ga wannan wata.

Ana sa ran, taron zai mai da hankali ne wajen lalibo bakin zaren hanyoyin da za su bunkasa shirin samar da abinci a Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China