in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayoyin Japan da wasu kasashe game da batun tekun kudancin Sin ba su dace da yanayin da ake ciki yanzu ba
2016-09-09 18:51:18 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Juma'a cewa, bisa muhimmin ci gaba da aka samu wajen aiwatar da sanarwar ayyukan bangarori daban daban game da batun tekun kudancin Sin da ka'idojin ayyukan da ya shafi tekun kudancin Sin da Sin da kasashen kungiyar ASEAN suka cimma, ra'ayoyin da Japan da wasu kasashe suka bayar game da batun ba su dace da yanayin da ake ciki a halin yanzu ba.

A dangane da ra'ayin da firaminstan kasar Japan Shinzo Abe ya bayar game da batun tekun kudancin Sin a gun taron kolin kungiyar kasashen gabashin nahiyar Asiya, Hua Chunying ta bayyanawa 'yan jarida cewa, a yayin taron kolin gabashin nahiyar Asiya da aka kammala, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun tekun kudancin kasar, kuma kasashe membobin kungiyar ASEAN sun goyi bayan wannan mataki. Yawancin kasashen sun yabawa Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN bisa kokarinsu na warware batun tekun kudancin Sin ta hanyar yin shawarwari, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin Sin a lokaci guda. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China