in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya bayyana matsayin Sin a kan kudancin tekun Sin a gun taron shugabannin Sin da kungiyar ASEAN
2016-09-08 10:08:11 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya halarci taron shugabannin kasar Sin da kungiyar ASEAN karo na 19 wanda ya gudana a cibiyar taro ta Vientiane dake kasar Laos, inda ya bayyana matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun tekun kudancin kasar.

A taron na safiyar jiya Laraba, Mr. Li ya bayyana cewa, bisa kokarin da kasar Sin da kuma kasashen ASEAN suka yi, yanayin batun kudancin tekun Sin ya samu kyautatuwa. Abubuwan da suka faru sun shaida cewa, sanarwar kudancin tekun Sin ta bangarori daban daban da kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN suka kulla na da matukar muhimmanci.

Ya ce a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, kasar Sin da kasashen ASEAN sun kiyaye zaman lafiya a yankin, kamar yadda sanarwar ta kayyade, kana kasashen da batun ya shafa sun bi ka'idar daidaita batun ta hanyar shawarwari cikin lumana. A halin yanzu kuma, kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN, na kokarin tattaunawa game da ka'idojin daidaita batun kudancin tekun Sin, domin kawar da sabani, da inganta hadin gwiwa.

A gun wannan taro, za a zartas da ka'idar dandalin diplomasiyya na daidaita batutuwan gaggawa na teku a tsakanin Sin da kasashen kungiyar ASEAN, da kuma hadaddiyar sanarwar amfani da ka'idojin gamuwar jiragen ruwa a kudancin tekun Sin, wadanda ke da muhimmiyar ma'ana ga kara amincewa da juna, da rage hadarin teku, da kiyaye zaman lafiya a kudancin tekun Sin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China