Shen Jinke ya yi bayani cewa, ayyukan da sojojin saman da aka tura suke gudanarwa sun hada da yin bincike ta sama, da yaki ta sama, da yin sintiri a tsibirai. Mr Shen ya kara da cewa, aikin sintirin da sojojin saman suke gudanarwa a tekun kudancin kasar Sin zai kasance aikin yau da kullum.
Shen Jinke ya bayyna cewa, sojojin saman kasar Sin sun yi aikin sintiri don sa kaimi ga raya horaswar yin yaki a kan teku, da karfin tinkarar kalubalen kiyaye tsaro, da tabbatar da ikon mallakar kasar da tsaron kasar. (Zainab)