Li Mingjiang ya bayyana cewa, bayan da aka gabatar da hukuncin da aka yanke game da batun tekun kudancin Sin, kasashen da abin ya shafa sun yi hakuri. Yanzu haka hukuncin ba zai yi wani babban tasiri ga halin da ake ciki a tekun kudancin kasar Sin ba.
A ganin Li Mingjiang, a shekarun baya baya nan, Sin da Philippine sun yi mu'amala da juna, idan suka yi shawarwari, wannan abu ne mai kyau a gare su. Gwamnatin Benigno Aquino III ta kasar Philippine da ta gabata ba ta yi amfani da matakan diflomasiya wajen tuntubar bangaren kasar Sin ba. Amma yanzu sabuwar gwamnatin kasar Philippine tana nuna fatan yin shawarwari, an yi imani da cewa, hakan zai taimaka wajen kara yin mu'amala a tsakanin Sin da Philippine. (Zainab)