in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin canza halayen 'yan kasa mai taken "Change Begins With Me'
2016-09-09 09:31:46 cri

Ranar Alhamis 8 ga wata ne, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani muhimmin shiri na sauya tunanin 'yan kasa mai taken "Change Begins With Me" a turance, wato canji ya fara daga ni. 

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wannan shiri ne a fadar shugaban kasa wato Aso Rock Villa dake Abuja, a ranar Alhamis da safe, inda aka samu halartar manyan jami'an gwamnatin Najeriya, ciki har da ministoci da dama, da gwamnoni, da jakadun kasashen waje dake Najeriya, da kuma 'yan jaridu na gida da na waje.

Shirin canza tunanin 'yan kasa mai taken "Change Begins With Me", wanda ke karkashin ma'aikatar watsa labarai da inganta al'adu ta tarayyar Najeriya, zai dinga fadakar da jama'a kan gyara halayensu, da nuna kishin kasa, da bada gudummawarsu da bin doka da oda ta kowane fanni don yin aiki tukuru, tare da zummar ciyar da kasar Najeriya gaba.

A wajen taron, aka kuma nuna wani hoton bidiyo mai ban sha'awa da kuma rera wata waka tare da yin raye-raye, don yin kira ga al'ummar Najeriya da su gyara dabi'unsu, da yaki da cin hanci da rashawa, da bada taimako wajen gina kasar Najeriya baki daya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China