Mahukuntan Najeriya sun yi watsi da rade radin da ake yi cewa za a kara farashin man fetur a kasar. A baya bayan nan dai wasu kafofin yada labaran kasar sun rika yada wasu rahotanni da ke cewa, sakamakon karancin kudaden musayar kasashen waje da ake amfani da su wajen sayo tatattaccen mai, gwamnatin Najeriyar na shawarar kara farashin man ga al'ummar kasar.
Da yake karin haske game da hakan, jim kadan bayan kammala tattaunawar sa da shugaban kasar Muhammadu Buhari, karamin ministan albarkatun man kasar Ibe Kachikwu, ya ce rahotannin da ake yadawa ba su da tushe bare makama.
Shi ma a nasa tsokaci game da wannan batu, babban manajan daraktan kamfanin sarrafa albarkatun man kasar NNPC Maikanti Baru, cewa ya yi NNPC ba shi da wani shiri na kara kudin man.(Saminu)