in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da jita jitar shigo da nau'in shinkafa daga kasashen waje
2016-09-08 09:42:17 cri

A jiya Laraba gwamnatin Najeriya ta karyata rahotannin da ake bazawa cewa ta shigo da nau'in shinkafa da aka sauyawa kwayoyin hallita daga kasashen ketare.

Rahotannin da ake bazawa a shafuka sada zumunta na zargin gwamnatin cewa, ta yi amfani da wasu kamfanonin kasar inda ta cika kasuwannin kasar da nau'in shinkafa 'yar waje da aka sauyawa kwayoyin hallita.

Rufus Ebegba, babban daraktan hukumar kula da lafiyar tsirrai ta kasar NBMA, ya shedwa taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, maganganun da ake yadawa babu kamshin gaskiya.

Ebegba ya ce, babu wata nau'in shinkafa 'yar waje da aka sauyawa kwayoyin hallita da aka shigo da ita kasar a hukumance, ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta sanya takunkumin shigo da shinkafa daga kasashen waje, kuma babu wasu alamu dake gwada cewa, an dage wannan takunkumi.

Ya ce, ana yada wannan jita jita ne domin haddasa matsaloli a kasar, don haka ya bukaci al'ummar Najeriya da su yi watsi da wadannan maganganun.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China