in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta bunkasa kimiyyar sararin samaniya domin ci gaban tattalin arzikin kasar
2016-08-30 10:39:06 cri
Gwamnatin Najeriya ta bayyana a jiya Litinin cewa, a shirye take ta bunkasa ci gaban kimiyyar sararin samaniya a matsayin hanyar da za ta habaka ci gaban tattalinn arzikin kasar.

Ministan kimiyya da fasaha na kasar Ogbonnaya Onu, ya bayyana a wajen bude taron shekara shekara game da kimiyyar sararin samaniya karo na 16 da aka gudanar a Abuja, ya ce, kimiyya da fasaha hanyoyin ne da za su samarwa kasar kudaden shiga a maimakon dogara kan albarkatun man fetur a matsayin hanya daya tilo ta samun kudin shigar kasar.

Taken taron na bana shi ne "kimiyyar sararin samaniya a matsayin hanyar dogaro da kai don samun ci gaba."

Ministan ya ce, Najeriya za ta yi amfani da kimiyyar sararin samaniya domin inganta samar da abinci, da ci gaban fasahar sadarwa, da harkar kiwon lafiya domin ci gaban kasar.

Ya kara da cewar, "ba za mu ci gaba da dogaro kan kasashen duniya ba, dole ne mu tashi tsaye domin samarwa kanmu mafita don mu tsaya da kafarmu".

Onu, ya ce, kimiyyar sararin samaniya za ta ingantawa kasar harkokin aikin gona wajen tafiyar da filayen noma, da maganin kwari, da noman rani domin samarwa kasar wadataccen abinci.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China