in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Najeriya na farautar masu garkuwa da ma'aikatan mai
2016-09-06 09:40:51 cri

A jiya Litinin hukumar 'yan sandan Najeriya ta sanar da aniyarta ta ci gaba da farautar wadanda suka yi garkuwa da ma'aikatan kamfanin mai 15 a Juma'ar da ta gabata, a jihar Kogi mai arzikin mai.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Nnamdi Omoni ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin fatakwal cewa, tuni hukumar 'yan sanda ta umarci jami'anta dake yaki da masu yin garkuwa da mutane, da sauran jami'an aikin tsaro na musamman domin kubutar da ma'aikatan man.

Wasu mutane dauke da makamai ne, suka yi awun gaba da ma'aikatan man 14 da kuma direbansu a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa yankin Omoku-Elele a jihar.

Omoni ya ce, kawo yanzu, sun gano motar da take daukar ma'aikatan zuwa wajen aikin, kana suna ci gaba da kokari domin ceto su ba tare da an yi musu wata illa ba, sai dai bai yi cikakken bayani game da yadda aikin kubutar da ma'aikatan man ke gudana ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China