in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan Atletico Griezmann ya danganta makomarsa da Simeone
2016-09-07 19:22:00 cri
Dan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann, ya tabbatar da makomarsa a kungiyar da yake takawa keda karkashin kociyan kungiyar Diego Simeone.

Griezmann, wanda shi ne ke kan gaba wajen zura ma kungiyarsa kwallaye a gasar zakarun nahiyar turai ta lokacin zafi, ya sake sabunta kwantiraginsa da kungiyar ta Atletico, inda ya amince zai cigaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2021, kan sabon farashin da ya kai kimanin euro miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 110.

To sai dai, kulub din Manchester United ya sayi takwarorinsa, kamar su Paul Pogba, hakan ya nuna cewa sayen nasa ba zai kasance wata barazana ba ga kuloflikan da suka fi arziki a Ingila, kuma a 'yan kwanakin da suka gabata, kafofin watsa labaru na Ingila sun danganta kulub din United da shi Griezmann.

Da yake zantawa da wani dan jarida ta shirin telabijn na Telefoot, Griezmann, yace, yana farin cikin cigaba da zama tare da Atletico Madrid, sai dai ya bayyana cewa makasudin zaman nasa a kulub din shine, domin ya cigaba da yin aiki da kociyan sa.

Dan wasan ya ce: "na kira shi kafin na rattaba hannu kan kwantiragi na, kuma ya tabbatar mini cewa zai ci gaba da aiki da kungiyar wasan. Abu ne mai muhimmanci a gareni na yi aiki a kulub din da kociyan sa yake da tabbaci a kaina. Ina farin cikin zamana a Spain, kuma zan koyi abubuwa masu yawa daga wajen Simeone. Zan iya samu shakku ne kadai idan ya kasance ya koma Paris Saint Germain, ko wani waje na dabam". " Zan cigaba da aiki a kulub din ne saboda ina son na yi aiki tare da Simeone. Hankali na zai iya tashi idan har ya bar kungiyar ta mu," ya riga ya furta hakan da bakinsa, duk da cewa hakan bai bayar da tabbaci mai yawa ba ga magoya bayan kungiyar ta Atletico.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China