Kanu wanda yanzu haka ya kai shekaru 40 da haihuwa ya nuna bajimta a wasan, wanda aka tashi Arsenal na da kwallo 4 Milan Glorie kuma na da 2.
Duk da kasancewar ya shiga wasan bayan kusan rabin sa'a da take leda, Kanu ya gwada irin basirar da yake da ita a wasan tamaula, inda ya zura kwallon sa ta farko jim kadan da shigar sa wasan.
Da yake bayyana irin farin cikin sa bayan kammala wasan ta shafin yanar gizon kungiyar, Kanu ya ce wasan ya sanya shi nishadi, duba da yadda ya ba shi damar taka leda da kuma faranta ran 'yan kallo da masu goyon bayan kungiyar.