Dan wasan na Brazil, wanda ya samu matsayi na bajinta a Camp Nou, bayan da ya taimakawa Blaugrana ta dawo da matsayinta, a wannan karo ma zai sake yin aiki tare da kungiyar. An ce, Barcelona ta bude wani sabon ofis a birnin New York na kasar Amurka a ranar 6 ga watan Satumba, domin neman kara samun karbuwa a duniya, hakan ne ya sa suka sake dawo da Ronaldinho.
Ana sa ran kungiyar wasan zata amsa sunanta, matukar hasashen da aka yi game da Ronaldinho ya kai ga nasara, a yayin da zai yi matukar kokarin tallafawa kolub din kamar yadda ya yi a baya.(Ahmad)