Wasan dai daya ne daga wasannin share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Najeriya da Tanzaniya da Masar ke bugawa a rukunin G, tuni kuma Masar ta samu gurbin gasar, don haka Tanzaniya da Najeriya na buga wannan wasa ne a matsayi na cikon wasanni kawai.
A wasan na garin Uyo dake jihar Akwa Ibom, Kelechi Iheanacho ya ciwa super Eagles din kwallo ne a minti na 79, gaban dubban 'yan kallo masoya kungiyar Super Eagles. Shi ne kuma wasan farko da sabon kocin Najeriyar Gernot Rohr ya samu nasara tare da kungiyar. Ana dai kallon wasan a matsayin wata dama da koci Rohr ya fara amfani da ita, wajen fara gwajin 'yan wasan kungiyar, don share fagen fara wasannin neman gurbi a gasar cin kofin duniya na shekarar 2018, wanda za a gudanar a kasar Rasha tun daga watan Oktobar shekara ta 2018.
Mai tsaron gidan Tanzaniya Aishi Manula, ya tsare kwallaye da dama daga 'yan wasan gaban Najeriya irin su Captain Mikel Obi, da Victor Moses da Muhammed Musa, kafin Kelechi Iheanacho ya samu damar ciwa Najeriyar wannan kwallo. A nata bangare, Tanzania ta kai hare hare da dama, sai dai 'yan wasan ta sun gaza jefa kwallo a ragar Najeriya.
Kungiyoyin kasashen biyu sun fara haduwa ne a shekarar 1973, a karo na biyu na gasar nahiyar Afirka, inda najeriya ta doke Tanzaniya da ci 2 da 1. A shekarar 1980 ma kungiyoyin biyu sun sake haduwa a wannan gasa karo na 12, inda Najeriya ta ci Tanzaniya 3-1. Kungiyoyin sun kuma hadu a wasannin share fagen gasar cin kofin duniya na kasar Sifaniya a shekarar 1982, da gasar nahiyar Afirka ta 1986. Tanzaniya dai bata taba doke Najeriya a wasan kwallon kafar ba.
Yanzu haka Super Eagles din za ta buga sauran wasannin ta ne da kungiyar Chipolopolo ta Zambia a birnin Lusaka, a ranar 3 ga watan Oktoba, cikin wasannin neman gurbin buga gasar cin kofin duniya na kasar Rasha dake tafe a shekara ta 2018.