Lamarin dai ya afku ne a lokacin horon na musamman da 'yan wasan ke yi a gaban jama'a, wanda ya samu halartar 'yan kallo kusan 15,000 a filin wasa na Amazonia.
A lokacin da lamarin ya faru, Neymar yayi kokarin buga wata kwallo ne, sai kawai wasu gungun magoya bayan kungiyar suka kutsa kai cikin filin wasan, kana daya cikin su ya rungumi Neymar ya kuma kada shi kasa.
Dan wasaan mai shekaru 24 da haihuwa, ya kwaci kansa daga hannun mutumin cikin sauri, kana ya fice daga filin wasan cikin murna tare da abokan wasan sa.
Yanzu haka kungiyar kwallon ta Brazil tana buga wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya. Kuma kungiyoyin shiyyar 4 dake kan gaba ne za su samu damar buga gasar da za a gudanar a shekarar 2018 a kasar Rasha. (Ahmad)